Tarrayar turai ta aike da wata tawaga zuwa Nigeria

Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega

Tarayyar turai ta aike da wasu masu sa ido hamsin da biyu zuwa Najeriya gabannin babban zaben kasar da za'a gudanar a watan gobe.

Ana saran jami'ai masu sa ido kimanin mutum dari da biyu ne daga nahiyar turai zasu iso Najeriyar kafin a fara zabubbukan kasar daga ranar biyu ga watan Aprilu, inda 'yan kasar zasu zabi 'yan Majalisun dokoki da shugaban kasa da kuma gwamnonin jihohi da ake saran kammalawa a tsakiyar watan.

Wadanda suka sa ido a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Najeriyar a shekarar 2007 sun bayyana zaben da cewa yana cike da kura kurai.

Sai dai a wannan karo, wasu kafafen yada labaru na cikin gida sun yi hasashen cewa mai yiwuwa zaben shugaban kasar kan iya kaiwa ga zagaye na biyu, wanda zai kasance na farko a tarihin kasar.