Bamu da niyyar kaiwa Gaddafi hari-Birtaniya

richard
Image caption Hafsan Hafsoshin Birtaniya, Sir David Richards

Kasashen Birtaniya da Faransa sun ce ba niyyarsu bace su kaiwa Kanal Gaddafi hari , a hare haren da suke kaiwa ta sama a Libya.

Hafsan hafsohin Birtaniya, Sir David Richards ya ce kai hari kan shugaban Libyan ba ya cikin kudurin Majalisar Dinkin Duniya na bada ikon daukar matakin soji domin kare fararen hula a Libya.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Faransa kuma ya jaddada cewa ko da an san inda Kanal Gaddafi yake baza'a kai masa hari ba.