'Yan sanda sun yi harbi a birnin Jos

police
Image caption 'Yan Sandan Najeriya

Rahotanni daga jos babban birnin Jihar Filato Najeriya na cewa jami'an tsaro sun yi harbe-harbe na kan mai uwa da wabi a yayin da dantakarar shugaban kasar jam'iyyar adawa ta CPC janar Muhammadu Buhari ke gudanar da gangamin yakin neman zabe yau a birnin.

Bayanai na nuni da cewa jami'an tsaron sun killace wasu manyan titunan birnin na Jos, inda suke hana mutane wucewa.

Jam'iyyar adawa ta CPC dai ta zargi gwamnatin jihar Filaton da kuma jami'an tsaro da hadin baki domin muzguna wa magoya bayanta.

Rahotanni dai sun bayyana cewa rundunar 'yansandan jihar Filato ta shawaraci jam'iyyar ta CPC da ta jinkirta gangamin yakin neman zaben nata na Jos saboda shi ma gwamnan jihar Jonah Jang na gudanar da nasa gangamin a yau, amma jam'iyyar bata yarda da hakan ba.