Ana ci gaba da gwabza fada a Libya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garin Benghazi

Ana ci gaba da gwabza fada ta kasa a Libya duk kuwa da hare hare ta sama da jiragen yakin kasashen yamma suka kaddamar akan sojojin kanar Gaddafi.

Akalla mutane tara ne aka bada rahoton cewa sojojin kanar Gaddafi sun hallaka a Misrata, daya daga cikin biranen da 'yan tawaye ke da karfi.

Bugu da kari a daren jiya litinin an ta jin karar bindigogi masu harbin jiragen sama a Tripoli babban birinin kasar.

Hukumomin Libya sun ce an kaiwa wani sansanin sojin jiragen ruwa da kuma wani kauyen masunta dake kusa da birnin Tripol hari.

A garin Benghazi kuma mutane da dama sun sami raunuka yayinda da wasu sun hallaka.

Duk da cewa gwamnatin Libya ta yi shellar tsaigata wuta kawo yanzu dakarun gwamnati na ci gaba da kaiwa yan tawaye hari a gabashin kasar kuma suna kokarin ganin cewa yankunan da suka kwace sun ci gaba da kasancewa karkashin ikonsu.