Najeriya ta soki kasashen yamma

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast

Gwamnatin Najeriya ta soki matakin da kasashen yamma suka dauka akan Libya.

Ta ce kaddamar da hare hare akan Libya tamkar an bar jaki ne ana bugun taiki.

Ministan harkokin wajen Najeriya Odein Ajumogobia ne ya bayyana haka inda ya ce abin takaici ne yadda kasashen duniya suka zura ido ana kashe farar hula a Ivory Coast tun bayan zaben da aka gudanar a watan Nuwamba bara.

A watan daya gabata ne dai Mr Ajumogobia ya ce tilas Majalisar dinkin duniya ta amince da duk wani irin matakin karfi, wajen hambarar da Laurent Gbagbo.

A cewarsa, hana gwamnatin Laurent Gbagbo damar shigowa da muhimman abubuwa da suke bukata shi ya kamata, idan hanyoyi lalama sun gaza.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa akalla mutane dari hudu da arba'in ne suka mutu sakamakon tashe tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar Ivory Coast da ake takaddama akai.