An yankewa tsohon shugaban Isra'ila hukuncin dauri

Moshe Katsav Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Moshe Katsav

A Isra'ila, kotu ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Moshe Katsav, hukuncin daurin shekaru bakwai a kurkuku.

Kotun ta same shi da laifin yin fyade da kuma matsa wa mata bisa neman alfasha.

Mr Katsav, wanda ya sauka daga shugabancin kasar a shekara ta 2007, ya musanta zargin da ake yi masa.

Kotun ta amince ta jinkirta daure shi har nan da wata guda, domin a bashi damar ya daukaka kara.