An kashe wani Mai Unguwa a Maiduguri

Birnin Maiduguri Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Maiduguri

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige wani Mai Unguwa a Maiduguri, tare da jikkata wasu mutanen biyu.

Lamarin ya faru a daren jiya a Unguwar Umarari dake yankin Karamar Hukumar Birnin Maiduguri da kewaye.

Birnin Maidugurin na ci gaba fuskantar hare hare da kashe-kashe.

A makon da ya gabata wasu 'yan bindiga suka hallaka wani Malami a unguwar Gomari, jim kadan bayan fitowarsa daga Masallaci, da kuma wasu mutane biyu a unguwar Maduganari.

Tun daga watan Yulin bara ne lamarin ke cigaba da tabarbarewa, musamman yanzu da ake fuskantar babban zabe a Najeriyar, duk kuwa da irin matakan tsaron da hukumomi ke ci gaba da dauka.