Kayan agaji ya kusa karewa a Ivory Coast

Yaran da rikicin Ivory Coast ya raba da gidajensu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yaran da rikicin Ivory Coast ya raba da gidajensu

Kungiyoyin ba da agaji a Ivory Coast sun yi gargadin cewa karfinsu na daf da karewa a yunkurin da suke yi na taimakawa mutanen da ke gujewa tashe-tashen hankula a kasar.

Kungiyoyin agajin sun ce in har ba su samu karin gudummawar kudi ba, to ba za su iya ci gaba da tallafawa dubban mutanen da ke tserewa daga babban birnin kasar, Abidjan, ba.

Ya zuwa yanzu dai dala miliyan bakwai ne kacal ya shiga aljihun gidauniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar tana neman dala miliyan talatin da biyu don agazawa wadanda fadan ya raba da gidajensu.

Wata jami'a a Ofishin Kula da Ayyukan Agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Elizabeth Byrs, ta ce bai kamata a manta da rikicin kasar ta Ivory Coast ba.

“Ya kamata kasashen duniya su mayar da hanakali ga kasar Ivory Coast saboda mutanen na bukatar taimako nan take”, in ji jami’ar.

Ta kuma kara da cewa, “Akwai mutane kusan dubu dari bakwai da rikici ya tilastawa barin Abidjan.

“A cikinsu akwai yara da matan da ke fafutukar ciyar da iyalansu”.

Majalisar ta Dinkin Duniya dai ta ce abincin da ta tanada don 'yan gudun hijira a kasashen Liberia da Ghana zai kare nan da 'yan watanni.