Japan: Tururin nukiliya a famfo ya ragu

Wata mata a Japan tana amfani da ruwan kwalba wajen girki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata mata a Japan tana amfani da ruwan kwalba wajen girki

Hukumomin birnin Tokyo sun ce yawan tururin nukiliyar da ke cikin ruwan famfo ya ragu; kuma hakan na nufin cewa a yanzu yara kanana za su iya shan ruwan.

Gargadin farko da aka yi game da yawan tururin nukiliyar da ke cikin ruwan famfo dai ya sa mutane sun yi ta rububin sayen ruwan kwalba, ita kuma gwamnati ta shirya raba ruwan kwalbar ga iyalan da ke da yara 'yan kasa da shekara guda.

Kuma yanzu haka ana ci gaba da kokarin dawo da wutar lantarki da kuma rage tafasar da tashar nukiliya ta Fukushima ke yi.

A halin da ake ciki kuma, mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadurran Nukiliya ta Japan, Fumio Matsuda, ya ce tururin nukiliyar ya shafi wadansu ma’aikatan agajin gaggawa su uku, biyu daga cikinsu ma na kwance a asibiti.