Shugaba Gaddafi ya yi jawabin bijirewa

Daya daga cikin magoya bayan Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Daya daga cikin magoya bayan Kanar Gaddafi

Gidan talabijin na gwamnatin Libya ya nuna Shugaba Muammar Gaddafi yana jawabi ga al'ummar kasar.

Wannan ne dai karo na farko da Kanar Gaddafi ya bayyana a bainar jama'a tun bayan da kasashen Yamma suka kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Libya ranar Asabar.

A jawabin na bijirewa, wanda ya yi a birnin Tripoli, Kanar Gaddafi ya shaidawa dimbin magoya bayansa cewa a karshe dai su ne za su yi nasara a kan 'yan tawayen kasar da kuma sojojin kawancen da Amurka, da Faransa, da kuma Burtaniya ke yiwa jagoranci.

A cewarsa al'ummar Libya kariya ce daga hare-haren da ake kaiwa kasar ta sama.

“Jama'a ne kariya mafi karfi daga hare-hare ta sama.

“Ga jama'ar a nan, kuma ga Gaddafi a tsakiyar jama'a.

“Wannan ne kariya daga hare-hare ta sama”, in ji Kanar Gaddafi.

Shugaban na Libya ya kuma ce wannan wani sabon yaki ne da kasashen Yamma suka daura da addinin Musulunci, sannan ya yi kira ga dukkan Musulmi su shiga yakin.

Sai dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki-Moon, ya yi kira ga dakarun Libya su ajiye makamansu, yana mai cewa Gaddafi shi kadai bai isa ya tunkari kasashen duniya ba har ya yi nasara.

Karin bayani