Za a soma kai hari a sojin kasa na Libya

Jiragen sama na yaki
Image caption Ghana ta koka a kan hare-haren

Kwamandan jiragen yakin Birtaniya da ke shawagi a saman kasar Libya ya ce yanzu dakarun sojin kasashen yamma ne ke iko da sararin samaniyar kasar.

Air Vice Marshal Greg Bagwell ya ce yanzu za su iya cin karansu ba babbaka, yayin da dakarun saman Kanar Gaddafi ba sa tashi.

Ya ce’ “Yanzu muna kara sa matsin lamba ba kakkautawa kan sojojin Libya. Ba su da wani katabus yanzu a wajen.”

Hafsan hafsoshin Amurka a Libya ya ce suna kara sa matsin lamba kan sojojin Gaddafi da ke kasa, wadanda ke barazana ga wasu birane.

To a baya-bayan nan dai, wasu shugabannin kasashe da kungiyoyi, sun rika bayyana rashin gamsuwarsu da matakan sojan da ake dauka a kan Libya, da sunan Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar Ghana ta bi sahun masu nuna rashin amincewa da salon hare-haren.

A hirar da ya yi da manema labarai jiya a birnin Accra, Ministan Harkokin Wajen kasar,

Alhaji Mohammed Mummuni, ya ce, ko da ya ke Ghana ta yi na'am da kudurin majalisar dinkin duniyar, amma ba ta jin dadin yadda ake ta kai hare-haren a Libya.