A shirye Najeriya take ta gudanar da zabe?

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Yayin da zabe ke kara matsowa, Kungiyar Lauyoyin Najeriya ta shirya wata tattaunawa mai taken “Shin a Shirye Najeriya take ta Gudanar da Zabe”?

Masu ruwa da tsaki a harkar zabe a kasar dai, wadanda suka hada da hukumar zabe mai zaman kanta, da lauyoyi, da kuma masu sa ido a kan zabe, da jami'an tsaro sun tafka muhawara tsakaninsu dangane da shirye-shiryen zaben da irin rawar da kowannensu zai taka da kuma kalubalen da ke gabansu.

Mataimakin Sufeto-Janar na ’yansandan Najeriya Azubuko Udah ya shaidawa BBC cewa, “Rundunar ’yansanda ta shirya tsaf; dangane da tashe-tashen hankulan da ake ta fama das u kuwa, wannan wata dabi’a ce ta ’yan siyasarmu ta ko a mutu ko a yi rai”.

Mista Udah ya kara da cewa a kasashen da suka ci gaba ba a ma bukatar ’yansanda su zo don tabbatar da an yi gaskiya.

“Amma ina tabbatar maka da cewa wata rana mu ma za mu yi ci gaban da ba sai mun bukaci dan sanda ba”.