Firayim Ministan Portugal ya yi murabus

Jose Socrates Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon Firayim Ministan Portugal, Jose Socrates

Firayim Ministan Portugal, Jose Socrates, ya ajiye aikinsa bayan majalisar dokokin kasar ta yi fatali da tsare-tsaren gwamnati na ceto tattalin arzikin kasar.

Gwamnatin kasar ta Portugal dai ta gabatarwa da majalisar dokokin wani shiri ne wanda ya kunshi tsuke bakin aljihu ta kowacce fuska da kuma karin kudin haraji da nufin shawo kan matsalar tattalin arzikin da kasar ta ke neman fadawa a ciki.

Da yake shaidawa manema labarai shawarar da ya yanke ta ajiye aikin nasa, Mista Socrates ya ce: “Daukacin jam'iyyun adawa sun yi watsi da matakan da gwamnati ta shirya dauka don hana Portugal karbo tallafin kudi daga waje.

“Saboda haka ne na mika takardar ajiye aikina na Firayim Minista ga Shugaban Kasa”.

Mista Socrates, wanda ya bayyana takaicinsa a kan yadda ya ce majalisar ta yi fatali da shirin gwamnatin, ya kuma ce shirin ya samu goyon bayan Hukumar Tarayyar Turai, da Babban Bankin Turai, da kuma abokan huldar kasar ta Portugal.

Kin da majalisar dokokin ta yi ta amince da shirin gwamnatin dai ka iya kara fargaba a kasuwannin hadahadar kudade dangane da ko Portugal za ta iya biyan basussukan da ake binta ba tare da ta samu tallafi daga waje ba.