Japan: Tururin nukiliya ya karu a teku

Firayim Ministan Japan, Naoto Kan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firayim Ministan Japan, Naoto Kan

Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta kasar Japan ta ce an gano sinadarin iodine mai dauke da tururin nukiliya a ruwan teku kusa da tashar nukiliya ta Fukushima, wadda girgizar kasa da mahaukaciyar igiyar ruwa ta tsunami suka lalata.

Yawan tururin nukiliyar da aka samu a tekun daura da tashar nukiliyar dai ya haura wanda aka samu a wurin a makon jiya sau takwas.

Hukumar ta ce babu kowa a gabar tekun, kuma tururin da aka gano ba zai zamo barazana ga rayuwa ba bayan kwanaki takwas.

Sai dai wannan abin damuwa ne; saboda ba ta tabbatar da ko ta ina tururin ya ke bulbulowa ba.

Mai yiwuwa tururin na kwarara ne ta cikin ruwan da ke karkashin kasa daga tukwanen nukiliyar da suka lalace.

An samu ruwa mai dauke da tururin da ya haura yadda ya kamata a samu har sau dubu goma a dakunan da tukwanen makamashin nukiliyar suke.

Jami'an hukumar dai na kokarin kwashe gurbataccen rowan; suna kuma kwarara ruwan da bai gurbata ba da nufin sanyaya tukwanen nukiliyar.

Karin bayani