An yi arangama a Amman babban birnin Jordan

Masu zanga-zanga a Jordan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Jordan

Daruruwan dalibai ne suka yi arangama da magoya bayan Sarki Abdallah na Jordan a tsakiyar babban birnin kasar, Amman, yayin wata zanga-zangar neman kawo sauyi a fagen siyasar kasar.

Rahotanni dai na cewa masu goyon bayan sarkin sun yi ta jifan masu zangar-zangar, wadanda suka yi sansani a tsakiyar dandalin Gamal Abdel Nasser.

An dai raunata da dama daga cikin masu zanga-zangar, kuma hakan ya sa an garzaya da wadansu daga cikinsu asibiti.

Yawancin masu zanga-zangar dai dalibai ne wadanda suka yi kiran a fito zanga-zangar ta shafin intanet din nan na zumunta, wato Facebook.