Amurka na taimakawa 'yan tawayen Libya

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Kafofin yada labarai na Amurka sun ba da rahotannin da ke nuna cewa hukumar leken asiri ta CIA ta tura jami'anta zuwa Libya.

Wadansu majiyoyin gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa makwanni biyu ko uku da suka gabata Shugaba Barack Obama ya rattaba hannu a kan wata takarda wadda aka fi sani da suna ‘abinda shugaban kasa ya gano’, wadda ta bayar da damar taimakawa 'yan tawayen Libya a fakaice.

Wannan takarda dai ta danganci ayyukan hukumur ta CIA.

Jaridar New York Times ta bayar da rahoton cewa hukumar ta CIA ta tura jami'anta kasar Libya, inda aka ce suna tattara bayanai don a kai hari ta jiragen sama, suna kuma tuntubar dakarun da ke adawa da Kanar Gaddafi.

Jaridar ta ce jami'an leken asirin Burtaniya ma na taka rawa a wannan aiki.

Wannan labari dai yana zuwa ne a daidai lokacin da ake muhawara a kan halalcin samar da makamai ga masu fada da dakarun Kanar Muammar Gaddafi.

A kafofin yada labarai dai Shugaba Obama ya ce ba za a aike da sojojin Amurka Libya ba, to amma ya ce yana duba yiwuwar samar da makamai ga 'yan tawayen.

Karin bayani