Ministan harkokin wajen Libya ya sauya sheka

Moussa Koussa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan harkokin wajen Libya, Moussa Koussa

Daya daga cikin makusantan Kanar Muammar Gaddafi ya koma Burtaniya.

Ministan Harkokin Wajen Libya, Moussa Koussa, ya sauka a Landan ne a wani jirgin sama wanda ake kyautata zaton na sojin saman Burtniya ne wanda ya tashi daga Tunisia, yana mai cewa ba zai sake wakiltar 'gwamnatin kama-karya' ba.

Shekara da shekaru dai Moussa Koussa ya kasance kusa a cikin gwamnatin Kanar Gaddafi.

An yi amannar cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen mayar da huldar diflomasiyya tsakanin Libya da kasashen duniya a shekarar 2003.

Ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen shirya tattaunawa mai cike da tarihi tsakanin Kanar Gaddafi da [Firayim Ministan Burtaniya] Tony Blair a shekarar 2004.

Hakazalika, an alakanta shi da tarwatsa jirgin saman nan na Amurka a garin Lockerbie a shekarar 1988; sannan da kitsa sakin mutumin da aka samu da laifin tarwatsa jirgin a bara.

Jami'an ma'aikatar harkokin waje da na leken asiri na Burtaniya sun yiwa Mista Koussa tambayoyi da fatan samun bayanan da za su taimaka wajen kawo karshen mulkin Gaddafi.

Zuwan Mista Koussa dai ya dace da lokacin da gwamnatin Burtaniya ta umurci wasu jami'an diflomasiyyar Libya su biyar su fice daga kasar a cikin kwanaki bakwai saboda kasasncewarsu barazana ga tsaron kasa.

Ana dai kyautata zaton cewa jami'an na barazana ne ga 'yan kasar Libya mazauna Burtaniya.