NATO za ta jagoranci kai hari kan Libya

Anders Fogh Rasmussen Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Sakatare Janar na NATO, Anders Fogh Rasmussen

Kungiyar tsaro ta NATO ta amince ta karbi jagorancin aikin tabbatar da haramacin tashin jiragen yaki a kasar Libya.

Jakadun kasashen da ke kungiyar ne suka yanke shawarar a wajen wani taro a Brussels, bayan an shafe kwanaki ana ce-ce-ku-ce dangane da rawar da NATO za ta taka a matakin sojin.

Amurka, wadda a yanzu ta ke shugabantar aikin, tana so ta kakkabe hannunta daga jagorancin cikin dan kanakanin lokaci.

Ana sa ran kungiyar ta NATO za ta karbe ragamar nan da kwana daya ko biyu.

Tuni dai aka danka alhakin kula da takunkumin hana sayen makamai da aka kakabawa kasar ta Libya a hannun kungiyar.

Sai dai har yanzu ba a yanke shawara a kan wanda zai jagoranci bangare na uku kuma mafi muhimmanci a matakin sojin ba—wato hare-haren da ake kaiwa don kare farar hula.

Sakatare Janar na kungiyar NATO, Anders Fogh Rasmussen, ya ce jakadun kasashen da ke kungiyar suna tattaunawa a kan ko NATO za ta karbi ragamar.

Har yanzu dai ana nuna damuwa a kan abin da ka iya biyo baya idan wata kungiyar tsaro ta yammacin duniya ta jagoranci hare-hare a kan wata kasa ta Musulmi.

Saboda haka ne, kamar yadda rahotanni suka nuna, kasashen Burtaniya, da Faransa, da Turkiyya suka kulla wata yarjejeniya wadda za ta shirya hanyoyin da NATO za ta bi don karbe ragamar jagorancin yakin baki daya.

Abu mafi muhimmanci a yarjejeniyar shi ne aikin ya kasance a karkashin kulawar wata majalisa wadda za ta kunshi jakadu da ministoci daga kasashen NATO da kuma kasashen Larabawan da ke goyon bayan hare-haren.

Karin bayani