Wani Kwamitin dattawa na ganawa da shugabannin al'umomi

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Goodluck Jonathan

Wani kwamitin dattawan arewacin Nigeria da Dr Goodluck Jonathan ya kafa don kokarin shiga tsakani a rikice rikicen siyasa ya fara ganawa da shugabannin al'umomi a arewacin kasar.

Shugabannin na zagayawa yankin arewacin kasar ne domin ganawa da masu fada a ji kamar shugabannin addinai na musulmi da kirista.

Saidai wasu na ganin an kafa kwamitin ne domin kokarin kamun kafa a arewacin kasar ga Dr Goodluck Jonathan.

An dai nada tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojin Nigeria, Alhaji Abdussalami Abubakar domin shugabantar kwamitin wanda ya hada da tsohon ministan gona, Shettima Mustapha da Alhaji Bamanga Tukur da Alhaji Tanko Yakasai da kuma Alhaji Hassan Adamu, wakilin Adamawa.