Dakatar da shugabannin kananan hukumomi

Jonah Jang
Image caption Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang

Gwamnatin Jihar Filato ta bayar da sanarwar dakatar da shugabannin kananan hukumomin Kanam da Langtang ta Kudu.

Hakan dai ya biyo bayan takaddamar da ta shiga tsakanin shugabannin wadansu kananan hukumomi na jihar ta Filato ne da gwamnatin jihar sakamakon matakin da gwamnatin jihar ta dauka na dakatar da baiwa kananan hukumomin kason kudinsu daga gwamnatin tarayya, wanda kan bi ta hannun jihohi.

Mai baiwa Gwamna Jonah Jang na jihar shawara a kan harkokin yada labarai, Malam Dauda Lamba, ya shaidawa BBC cewa gwamnatin ta dauki matakin ne saboda tana zargin shuwagabannin kananan hukumomin da yin almubazzaranci da dukiyar jama'a.

“Shi ya sa Gwamna Jang ya ce dole ne a bincika wannan zargi a ga yaya za a yi don a kare mutuncin jama’ar Jihar Filato”, in ji Malam Dauda Lamba.

Shugabannin kananan hukumomin dai—na Kanam, da Langtang ta Kudu, da Langtang ta Arewa, da kuma Bokkos—wadanda ‘yan jam’iyyun adawa ne, sun musanta hakan, suna masu cewa matakin gwamnatin jihar zalunci ne a garesu da al’ummun kananan hukumomin nasu.