'Ba za mu shiga muhawarar BON ba'

'Yan takarar shugabancin Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Malam Ibrahim Shekarau, da Malam Nuhu Ribadu, da Janar Muhammadu Buhari

Wadansu 'yan takarar shugabancin Najeriya sun bayar da sanarawar kauracewa wata muhawarar talabijin wadda Kungiyar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Najeriya, wato BON, ta shirya tsakaninsu da Shugaba Goodluck Jonatahan, wanda ya ke takara a karkashin jam'iyyar PDP mai mulki.

Janar Muhammadu Buhari mai ritaya na CPC, da Malam Nuhu Ribadu na ACN, da Malam Ibrahim Shekarau na ANPP, sun ce ba za su shiga muhawarar wadda aka shirya yi a ranar 29 ga wannan wata ba.

Sule Ya’u Sule, wanda shi ne kakakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ANPP, Malam Ibrahim Shekarau, ya shaidawa BBC dalilinsu na kauracewa muhawarar.

“A gaskiya mu ba mu amince ba ne da tsarin da aka yi a wancan bangaren—wato, mu muna ganin kamar akwai wani abu da aka binne a kasa wanda mu ba mu sani ba, domin mutanen nan sun zo mana da bukata a [muhawarar da aka yi a baya]; bukatarsu ba ta samu shiga ba saboda haka suka ki shiga waccan muhawarar.

“Sai suka tafi wani waje suka ce za su yi a can; muna ganin kamar wannan abin da suka nema a nan ba su samu ba, kila sun samu a can”.

Sule Ya’u Sule ya kuma ce ba tsoro ne ya sa ‘yan takarar uku suka janye daga muhawarar ba: “Abin ne muka ga babu dimokuradiyya a cikinsa, domin idan da akwai dimokuradiyya, me ya sa [Shugaba Goodluck Jonathan] ya ki zuwa [muhawara ta] farko da aka shirya?”

A kwanakin baya dai wadannan 'yan takarar sun bayyana a wata muhawara wadda wani gidan talabijin mai suna NN24 ya shirya, wadda ba ta samu halartar Shugaba Goodluck Jonathan ba.

Su dai 'yan adawar sun yi zargin cewa a muhawarar farko, bangaren Shugaban kasar ya bukaci a fada masa tambayoyin da za a ayi a lokacin muhawarar.