Rikicin Ivory Coast na kara kamari

Yaran da rikici ya raba da gidajensu a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yaran da rikici ya raba da gidajensu a Ivory Coast

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, wato UNHCR, ta ce sojojin haya daga Liberia suna musgunawa al'umma suna kuma dibar ganima a yammacin kasar Ivory Coast.

Ko a makon nan mai karewa ma an fasa ofisoshin hukumar da kuma na wadansu kungiyoyin bayar da agaji da ke garin Guiglo.

Hukumar ta yi gargadin cewa al'ummar garin na Guiglo na kara fuskantar ta’addancin sojojin hayar, wadanda baya ga musgunawa mazauna yankin suke kuma kaddamar da hare-hare a kan cibiyoyin kasuwanci.

Tun bayan da kungiyar tsofaffin 'yan tawayen kasar mai suna New Forces ta karbe iko da kan iyakar kasar Ivory Coast da Liberia da nufin hana sojojin da Laurent Gbagbo ya hayo shiga kasar ne dai zaman dar-dar ya karu a yankin.

Ita dai kungiyar ta New Forces tana goyon bayan Alassane Ouattara ne wanda kasashen duniya suka ce shi ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamban bara.

A babban birnin kasar, Abidjan, kuma ana ci gaba da da samun tashe-tashen hankula yayinda magoya bayan Alassane Ouattara ke kara mamaye unguwannin Abobo da Anyama a arewacin birnin.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi kashedin cewa kasar Ivory Coast na fuskantar barazanar fadawa yakin basasa.

Ranar Alhamis kuma shugabannin kasashen ECOWAS suka kammala taronsu tare da yin kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya ya yi amfani da karfi ta halastacciyar hanya don kare farar hula da kuma dora Alassane Ouattara a kan kujerar mulki.