Neman yin waje da Laurent Gbagbo

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast

Bisa ga dukkan alamu a yanzu bakin shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar Ecowas ko Cedao, yazo daya, akan batun rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar Cote d'voire.

Shugabannin kasashen sun yi kira ga Kwamitin sulhu na Majalissar Dinkin duniya da ya dauki matakin tabbatar da ganin Laurent Gbagbo ya sauka daga kan karagar mulki.

Tun a farkon rikicin siyasar na Cote d'voire, Kungiyar Ecowas ta yi barazanar amfani da karfi, domin tursasawa Laurent Gbagbo ya sauka, amma wasu daga cikin kasashen kungiyar suka nisanta kansu da daukar irin wannan mataki.