Nijar ta kaddamar da sabon maganin zazzabin cizon sauro

Sauron da ke sa zazzabi
Image caption Sauron da ke sa zazzabi

A jamhuriyar Nijar, hukumomin kiwon lafiyar kasar ne tare da tallafin hukumar lafiya ta duniya, har ma da sauran kungiyoyi da kasashe masu hannu da shuni, suka kaddammar da wani sabon maganin yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Maganin mai suna ACT ya kunshi wasu nau'o'in magungunna daban-daban da suka hada da Amodiaquine.

Ana kyautata zaton maganin zai iya warkar da cutar zazzabin cizon sauro a cikin sa'o'i 72, kuma ana sayar da shi a farashi mai rahusa.

shugaban hukumar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta kasa, Dokta Abbani Maazou, ya fadawa BBC cewa maganin yana da inganci sosai saboda an gudanar da cikakken bincike a kansa.