Zaa kawo karshen harba makaman roka cikin Isra'ila

Barnar da jiragen yakin Isra'ila suka yi a Gaza Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barnar da jiragen yakin Isra'ila suka yi a Gaza

Kungiyar Hamas ta Falasdiinawa da sauran kungiyoyi a Zirin Gaza sun amince su dakatar da harba rokoki cikin Isra'ila, muddin ita ma Isra'ila ta dakatar da harin da take kaiwa a kan Zirin na Gaza.

An cimma yarjejeniyar ne a wata ganawa da nufin kwantar da kura tsakaninsu da Isra'ilar, bayan taho-mu-gamar da aka yi a 'yan kwanakin nan ta kai ga kisan Falasdinawan guda goma.

Kakakin majalisar dokoki, kuma dan kungiyar Hamas, Abdul-aziz Duaik, ya ce taron ya yi nasara, kuma zaa tabbatar cewa an yi aiki da 'yarjejeniyar.