An kashe wani shugaban jam'iyyar ANPP a Maiduguri

Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan sanda suna zargin 'yan Boko Haram da kai harin

Rahotanni daga Maiduguri Babban birnin jihar Borno dake Arewacin Najeriya sun nuna cewa a dazu da rana wasu yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyar ANPP na yankin unguwar Gwange, Alhaji Modu Gana Makanike.

Al'ammarin ya faru ne lokacin da yan bindigar, wadanda ake zargin 'yan Boko Haram, suka bude wuta a wani taron da 'yayan jam'iyar dake wannan yankin ke gudanarwa.

Ko a daren jiya ma rahotannin sun nuna cewar an yi ta musayar wuta tsakanin wasu 'yan bindiga da jami'an sojoji a Tashar Bala dake unguwar London Ciki a birnin na Maiduguri.

Wannan musayar wuta dai ta sa mazauna unguwar da dama sun tsere daga gidajen su.

An dai jima ana ta fama da kai hare-hare a birnin na Maiduguri, kuma jami'an tsaro na dora alhakinsu ne a kan 'yan Kungiyar Boko Haram.