Da alamun Angela Merkel ta sha mummunan kaye a zabe

Angela Merkel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angela Merkel

Sakamakon farko na zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Baden-Wuerttemberg a Jamus ya nuna cewa, shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel ta sha mummunan kaye.

Sakamakon ya nuna cewa, jam'iyyarta ta Christian Democrat za ta rasa mulki a jihar, wadda ta kasance a hannunta na tsawon shekaru 60.

Ministan harkokin wajen Jamus din, Guido Westerwelle, ya bayyana zaben da cewa wata kuriar raba-gardama ce a kan batun amfani da makamashin nukiliya.

A cewar masu nazari kan al'amura, cikakken goyon bayan da Angela Merkel ta rika baiwa batun samar da makamashin nukiliyar, kamin daga baya ta sauya matsayi sakamakon hadarin nukiliyar Japan, ya taimakawa jam'iyyar Green, ta masu fafutukar kare muhalli.

Ga alama dai 'yan kare muhallin ne za su kafa gwamnati a jihar a karon farko, idan suka yi kawance da jam'iyyar Social Democrat.