An lalata jiragen saman Libya

Jiragen saman Faransa a Libya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen saman Faransa sun lalata na Libya

Faransa ta ce jiragen samanta sun lalata jiragen sama guda biyar da masu saukar angulu guda biyu mallakin gwamnatin Libya a wani hari da aka kaiwa dakarun Gaddafi.

Wani kakakin gwamnatin kasar ya ce jiragen samansu sun lalata filin saukar jiragen sama a garin Misrata.

Bugu da kari , 'yan tawaye a gabashin Libya sun ce sun kwace iko a tashar samar da mai ta garin Brega, sai dai ba'a samu wani wanda ya tabbatar da hakan ba.

Daga bisani 'yan tawaye sun sake kwace garin Ajdabiya daga dakarun gwamnati kasar.