'Yan tawayen Libiya na ta samun galaba

'Yan tawayen Libiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Libiya

'Yan tawaye a Libya suna dannawa cikin sauri zuwa yammacin kasar, don tikarar sojojin dake biyaya ga Kanar Gaddafi.

'Yan tawayen dai na samun taimakon kasashen yammacin duniya dake kai hare-hare ta sama, a kan tankoki yaki da makaman atilare na sojojin gwamnati.

An ji karar fashewar abubuwa da kuma harbin makaman kakkabo jiragen sama a birnin Tripoli.

Haka zalika an ji karar fashewar abubuwa a birnin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafin.

Tun farko dai 'yan tawayen Libiyar sun kwace garuruwan Brega da Ras Lanuf mai tashar mai.

Sun ce, za su iya fara fitar da man zuwa kasashen waje a cikin kasa da mako daya.

Jakadun kasashen kawancen tsaro na NATO, sun amince kungiyar ta jagoranci dukan farmakin sojan da ake kaiwa Libiyar.