An gano nukiliya fiye da kima a Japan

Ma'aikata a tashar Fukushima Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gano sinadarin nukiliya fiye da kima a Japan

Ana sake fuskantar wata sabuwar fargaba a kasar Japan, inda girgizar kasa da Tsunami suka yiwa tashar nukiliya ta Fukushima illa.

Hakan dai na zuwa ne, a yayin da aka gano sinadarin nukiliya wanda ya zarta kima a wani bagare na tashar.

Hukumar da ke kula da tashar nukiliyar ta ce tururin ya zarta wanda aka gano a baya da fiye da kaso miliyan goma.

Hukumar ta ce mai yiwuwa tururin na fitowa ne kai tsaye daga tukunyar nukiliyar.