Syria ta ce mutane 12 ne suka hallaka a Latakia

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Gwamnatin Syria ta ce, mutane goma sha biyu ne aka kashe jiya Asabar, lokacin da tashin hankali ya barke, yayin da ake zanga -zangar nuna ma ta kyama, a birnin Latakia da ke gabar teku.

Akalla wasu mutanen dari biyu kuma sun jikkata, lokacin da wasu 'yan bindiga-dadi da ba a shaida ba, suka labe a saman gine-gine, suka yi ta harbin masu zanga zangar.

Jami'an Syriar suka ce, yawancin wadanda aka kashen, fararen hula ne da kuma dakarun tsaro.

Nan ba da jimawa ba ake sa ran shugaban kasar, Bashar al-Assad, zai yi wa al'ummarsa jawabi, bayan an kwashe fiye da mako guda ana ta zanga zangar adawa da gwamnati.