Sabuwar girgizar kasa a Japan

Ambaliyar ruwa a Japan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Irin barnar da girgizar kasa ta yi a Japan

An sake samun aukuwar girgizar kasa a gabar tekun Arewa maso gabashin Japan.

Karfin girgizar kasar ya kai maki shida da digo biyar, abin da ya sa jami'an kasar suka yi gargadin aukuwar ambaliyar ruwa ta Tsunami.

Sai dai sun ce a wannan karon karfin ambaliyar ruwan ba zai kai irin wanda ya yi matukar barna fiye da makonni biyu da suka gabata a kasar ba.

Hukumomin kasar na ci gaba da aikin kai agaji a yankunan da suka fuskanci sabuwar ambaliyar ruwan.