Sabuwar hanyar a kasa a tsare a Nigeria

Gangamin zabe a Nigeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gangamin zabe a Nigeria

Yayin da ya rage kasa da mako daya a fara gudanar da zabukan Najeriya, jam'iyyar CPC a jihar Jigawa ta bullo da wani tsari na horar da wakilanta, wadanda za su yi mata aikin sanya idanu a wuraren zabe.

Horon ya kunshi wani tsari ne na amfani da wayar salula da na'ura mai kwakwalwa wajen aikawa da sakonni a kan aikata magudin zabe.

A karkashin tsarin dai, jam'iyyar za ta samar da wata cibiya ce a hedikwatarta ta jihar, wadda za ta rinka karbar bayanan daga ko'ina daga sassan jihar, inda kuma za ta rika shedawa hukumomin da suka dace domin daukar matakan gaggawa don magance magudin zaben.