An yankewa mutane 18,000 hukuncin kisa

Tambarin Amnesty International
Image caption An kashe kimanin mutane 18,000, in ji Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya wato Amnesty International ta ce kimanin mutane18,000 ne aka yankewa hukuncin kisa a kasashen duniya a bara.

Kungiyar ta ce kawo yanzu China ita ce kasar da ta fi kashe mutanen da aka yankewa hukuncin kisa.

Sauran kasashen sun hada da Iran, da Koriya ta Arewa, da Yemen, da Amurka, da Saudiya da kuma Libya .

Kungiyar ta ce a kasashe da dama ana amfani da hukuncin kisa ta hanyar da bata dace ba akan marasa galihu da kuma al'ummomi marasa rinjaye.