Birnin Sirte na hannun dakarun Gaddafi

Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yan tawayen Libya

'Yan-Jarida da ke birnin Sirte na kasar Libya, sun ce har yanzu garin na hannun dakarun gwamnatin kasar, duk kuwa da ikrarin da masu hamayya da gwamnatin ke yi cewar sun kame garin.

Rahotanni sun ce sojojin Kanar Gaddafin wadanda ke amfani da bindigogin da aka girke a bayan akori kura, sun dakatar da dannawar da yan tawayen ke yi ta kan hanyar da ke bakin ruwa, wadda ke gabashin birnin.

Birnin na Sirte dai shi ne mahaifar Kanar Gaddafi, kuma wuri na karshe da ke hannun dakarunsa a waje da yammacin kasar.