Fada na kara bazuwa a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, a yanzu fadan da ake gwabzawa a Ivory Coast ya bazu zuwa sauran yankunan kasar daga birnin Abidjan, kuma dubun dubatar jama'a sun rasa na yi.

A birnin Geneva, wakilan kungiyoyin agajin sun ce, dubban mutane sun nemi mafaka a coci-coci da sauran gine-gine na hukuma.

Sai dai ba wani taimakon da ake basu.

Rikicin na Cote d'Ivoire ya barke ne bayan zaben shugaban kasar na watan Nuwamba, inda shugaba mai ci Laurent Gbagbo, da dan takarar adawa Alassane Ouattara, kowanensu ke ikirarin samun galaba.