Mutane miliyan biyu na bukatar agajin abinci a Nijer

Hukumomin Nijar sun bayyana cewa, kimanin mutane miliyan biyu ne suke bukatar abinci, sakamakon rashin kyawon daminar bara a wasu yankunan kasar.

A kan haka ne ma kwararru ta fuskar noma ke taro tun daga jiya, domin ganin yadda za a tinkari matsalar.

Rahotani sun ce, a jahar Damagaram kawai, ana fuskantar karancin cimaka a garuruwa kusan dari biyu da talatin.