Fargabar tashin hankali a zaben Najeriya

Taron siyasa a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana nuna fargaba kan zabe a Najeriya

Jama'a da dama a Najeriya na fargabar yiwuwar tashin hankali a lokacin gudanar da babban zaben kasar.

Mutanen da BBC ta yi hira da su sun ce yawan hare-hare da ake kaiwa magoya bayan mabambantan siyasu na damunsu

Sun yi kira ga hukumomin tsaro su dauki matakan magance rikicin da ka iya faruwa a lokacin zaben.

Tashin hankali a lokacin zabe dai ba bakon abu bane a Najeriya.

Yanzu haka dai hukumomin kasar sun mai da hankali ne akan kaucewa tashe-tashen hankula a lokacin zabe.

'Yan sanda da sauran jami'an tsaro na horar da jami'ansu akan dabarun karya-lagon masu neman kawo rikici.