Amurka za ta baiwa 'yan tawayen Libya makamai

Shugaba Barack Obama Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka za ta baiwa 'yan tawayen Libya makamai

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce mai yiwuwa kasarsa ta taimakawa 'yan tawayen Libya da makamai don ci gaba da gwagwarmayar da suke yi da dakarun Gaddafi.

A wasu jerin hirarraki da wani gidan talabijin din Amurka, shugaba Obama ya ce har yanzu yana nazari kan irin taimakon da 'yan tawayen Libya ke bukata daga wajensa.

Ya kara da cewa, takunkumi da kuma hare-haren da ake kaiwa dakarun Gaddafi sun yi matukar illa a gare shi.

Ya ce:''Ba ni da shakkun cewa, idan muna son shiga da makamai Libya, abu ne mai yiwuwa''.