Iraqi ta zargi 'yan Sunni da kisan mutane

Taswirar Iraqi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hukumomi sun zargi 'yan Sunni da kisa a Iraqi

Mahukunta a kasar Iraqi sun ce, sun yi imanin cewa mayakan Sunni ne da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda suka kai wani mummunan samame a jiya Talata.

Harin dai ya yi sanadiyar halaka mutane fiye da hamsin.

Tashin hankalin ya auku ne a karamar hukumar Tikrit, mahaifar tsohon shugaban kasar ta Iraqi Saddam Hussien.

Kazamin musayar wutar ya kawo karshe ne bayan da maharan kimanin mutane takwas suka tayar da bam din da ke jikinsu.

Daga cikin wadanda suka rasu akwai jami'an karamar hukumar da kuma wani dan jaridar Iraqi. A da dai, Tikrit na daya daga cikin matattarar mayakan Sunni.