Dakarun Ouattara sun kwace babban birnin kasar

Yantawayen dake goyon bayan Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yantawayen dake goyon bayan Ouattara

Mazauna babban birnin kasar Cote de 'Ivoire, Yamassoukro sun ce dakarun Alassane Ouattara, mutumin da duniya ke dauka a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar, sun kwace birnin dake da matukar muhimmanci a kasar.

Wakiliyar BBC tace wani mazaunin birnin Yamassoukro ya shaidawa BBC cewa dakarun Ouattara sun shiga birnin ba tare da wata tirjiya mai karfi ba.

Har ila yau rahotanni sun ce dakarun Mr. Ouattar, wadanke ke dannowa daga arewacin kasar sun kwace garin Soubre.

Sai dai kuma har yanzu yawancin birnin Abidjan, na hannun Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga mulki tun bayan zaben da akai a watan Nuwambar bara da ake ta takaddama a kai.

Yanzu haka ana cewa dakarun Mr. Outtara na ci gaba da dannawa zuwa tashar ruwan San Pedro, tashar da ake fitar da koko zuwa kasashen waje