'Yan tawaye sun shiga babban birnin Ivory Coast

Dakarun da ke goyon bayan mutumin da majalisar dinkin duniya ta amince da shi a matsayin zababben shugaban kasar Ivory Coast Allasane Ouattara sun shiga babban birnin kasar, kamar yadda wasu mazauna birnin na Yamoussoukro suka shaida wa BBC.

Sojojin Ouattara na dada nausawa arewa, kuma shugaba mai ci a yanzu Laurent Gbagbo ya yi rokon da a tsagaita bude wuta.

Mr Gbagbo ya ki ya sauka daga karagar mulki duk da cewa majalisar dinkin duniya ta ce ya fadi a zaben da aka gudanar a kasar a watan Nuwamban da ya gabata.

Abidjan ne birni mafi muhimmanci a Ivory Coast, sai dai wakilin BBC ya ce kame birnin Yamoussoukro zai zamanto wata nasara ga dakarun da ke biyayya ga Outarra.

Kimanin mutane miliyan daya ne i zuwa yanzu suka tserewa tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar, kuma akalla mutane 462 ne aka kashe tun watan Satumbar da ya gabata, in ji majalisar dinkin duniya.