Shugaba Goodluck yayi muhawararsa shi kadai

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya halarci wata muhawara shi kadai a taron muhawarar da wata kungiya mai suna Nigeria Debate Group ta shirya domin 'yan takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa.

Shugaba Goodluck Jonathan ya halarci muhawarar shi kadai ne sakamakon kauracewar da abokan hamayyarsa na jam'iyyun adawa na ACN, da CPC da kuma ANPP suka yi.

A baya an yi ta cece - ku ce a kan kauracewa irin wannan muhawara da wani gidan talabijin mai zaman kansa na NN24 ya shirya, inda manyan abokan hamayyarsa na ACN, da CPC da kuma ANNP suka yi muhawara a tsakaninsu, yayinda shi kuma shugaba Jonathan ya kaurace.

Wannan ya sa an yi ta yi masa surutai tare da cewar tsoro ne ya hana shi zuwa.