'Yan tawayen Libya na ci gaba da ja baya

'Yan tawaye a Libya na ci gaba da ja baya, yayin da dakarun gwamnati ke kara dannawa wuraren da suke.

Daruruwan mayakan 'yan adawar sun tsere daga garin Brega, inda ke da man fetur, yayinda tuni da ma suka bar wasu garuruwan dake gabar ruwa.

'Yan tawayen sun ce 'yan hare haren da dakarun kawance suka rika kaiwa ta sama kwanaki biyun da suka wuce ne suka ba dakarun gwamnatin wannan damar.

Wani wakilin BBC a Tripoli ya ce dakarun Kanar Gaddafi sun fara tuka manyan motoci da aka yiwa shimfida ta musamman dauke da manyan makamai, abinda zai yi wuya ga jiragen yakin kungiyar kawance su gane su.

A halin da ake ciki kuma, Gwamnatin kasar Libya ta ce za ta kai karar duk wani kamfanin mai na kasar wajen da ya sayi mai a hannun 'yan tawaye.

A mako mai zuwa ne 'yan tawayen ke fatan fara sai da man domin samun kudaden da za su tafiyar da ayyukan tada kayar bayan da suke.

Yanzu haka dai garuruwa biyu dake da man fetur da 'yan tawayen suka kama sun kubuce musu. Kasar Qatar ta ce za ta taimaka wajen sayar da man a kasuwannin duniya.