Shugaba Assad ya yi wa 'yan Syria jawabi

Shugaba Bashar Assad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Bashar Assad

A jawabinsa na farko ga kasa tun bayan da aka fara zanga zangar kin jinin gwamnati makwanni biyun da suka wuce, shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria ya yadda cewa wasu daga cikin bukatun masu zanga-zangar halatattu ne.

Ya kuma yarda cewa tilas ne ai sauye-sauye, amma bai bada jadawalin yadda za a yi su ba.

Mr Assad ya ce da yawan 'yan kasar Syria na neman sauye-sauye ne, suna da bukatunsu da ba'a biya musu ba, mun tattauna wannan kuma mun yi amannar ba'a cimmusu ba, mun kuma nemi abubuwa da dama daga 'yan kasar.

Mr Assad ya ce Syria na fuskantar wata makarkashiya da nufin karya lagwanta ga turjiyar da take wa Isra'ila, sai dai kuma ba duk mutanan da suka yi ta zanga-zangar ba ne ake hada baki da su.

Da yake jawabi a majalisar dokokin, ya bayyana cewa Syriyawa na bukatar sauye sauye, don haka sun nuna matukar goyan bayansu ga wannan bukata.

Kafin ya fara jawabin, muhawara a tsakanin 'yan kasar ta kara zafafa.

Akwai dai matukar hadin kai a tsakanin magoya baya da kuma 'yan adawa da shugaba Asad din kan cewa akwai bukatar yin sauye sauye ba tare da bata lokaci ba.

Shugaba Assad ya ce: "Mafi yawan al'ummar Syria na kira kan yin sauye sauye, dukkan ku masu son a yi sauyi ne. Al'ummar Syria na da bukatun da ba'a cika musu ba. Mun tattauna akan wannan kan cewa akwai bukatu da dama a bangaren al'ummar Syria. Sai dai kuma abubuwa da dama sun faru. Sun yi amfani da wannan sauye-sauyen da suke so a yi a matsayin madogara domin janyo al'umma kan tituna domin yin zanga-zanga, duk da dai cewa wasunsu na da kyakkyawar aniya."

Sai dai kuma akwai damuwa matuka a bangaren al'ummar Syrian kan cewa bayan wannan jawabin ba lallai bane ya kasance abubuwan da aka tattauna din su kai yanda ake zato ba.

Akwai kuma tambaya kan yadda za'a bi wajen aiwatar da su da kuma ko yaushe ne.

Akalla dai mutane sittin ne ake tunanin sun rasu a cikin makwanni biyu, an kuma kame mutane da dama a duk fadin kasar.

Sai dai kuma duk da haka zanga-zangar adawa da gwamnatin na ci gaba, musammman ma da yake ana tsammanin yin wani babban gangamin 'yan adawa ranar Juma'a mai zuwa.