Bam a wajen kamfen din Janar Buhari

Janar Mahammadu Buhari
Image caption Janar Mahammadu Buhari

An kwance wasu bama-bamai biyu da aka dasa a filin wasan da dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar CPC, ya gudanar da yakin neman zabensa yau a Katsina.

An gano bama-baman ne a filin Polo na birnin Katsinar, bayan da wasu daga cikin mutanen da suka taru, suka ankara da su.

Haka kuma, bayan da aka kallama taron a birnin Katsinar, Janar Buharin ya koma gidansa a Daura, wani al'amarin ya faru, inda wani dan sanda ya bindige wani mutum, yayinda jama'a ke kokowar shiga cikin gidan Janar din.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin.