Yau jajiberin manyan zabubbukan Najeriya

Taron hukumar INEC da jam'iyyun siyasar Najeriya
Image caption Taron hukumar INEC da jam'iyyun siyasar Najeriya

Yau ne jajiberin zabubbuka a Najeriya, inda ake sa ran mutane sama da miliyan saba'in da uku wadanda hukumar zaben kasar, wato INEC, ta yiwa rajista za su kada kuri'a.

Za a fara zabubbukan kasa baki daya ne dai gobe Asabar da zaben 'yan Majalisar Tarayya.

Kuma a yau din ne, ake kawo karshen yakin neman zaben da masu takarar mukaman 'yan Majalisar Tarayyar ke yi a duk fadin kasar.

Zabubbukan dai na zuwa ne a lokacin da al’ummar kasar da ma sauran kasashen duniya ke fatan za a yi bankwana da kurakuran da aka gani a zabubbukan baya, a gudanar da ingantaccen zabe.

Daya daga cikin hanyoyin da wadansu 'yan Najeriya ke ganin za a iya amfani da su wajen nadar duk wani yunkurin tafka magudi a rumfunan zabe dai ita ce ta hanyar amfani da wayoyin salula.

A kwanakin baya wadansu kungiyoyin da ke sa ido a kan yadda ake gudanar da zabubbuka a kasar sun kafa wata cibiyar tattara bayanan da za a nada ta hanyar amfani da wayoyin salula.

Kuma hukumar INEC ta sanar da wadansu layukan salula wadanda masu kada kuri’a za su iya amfani da su wajen aikawa hukumar sakwannin yadda ake gudanar da zabubbukan a mazabunsu.

A kwanakin baya dai rahotanni sun ce Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Hafizu Ringim, ya haramta amfani da wayar salula mai kamara a lokacin zabe, amma hukumar 'yan sadan ta musanta hakan.

Kakakin rundunar 'yansanda na kasa ya aikewa BBC wata sanarwa wadda ke cewa Babban Sufeton 'yan sandan, ko da wasa, bai taba haramta wa jama'a yin amfani da wayar salula mai kamara a runfunan zabe ba.