Dakarun Alassane Ouattara sun kai hari gidan Laurent Gbagbo

Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Laurent Gbagbo

A Cote d'Ivoire, dakaru masu adawa da shugaba Laurent Gbagbo da aka yiwa kawanya, sun kai hari a fadarsa, bayan tattaunawar da ake a kan neman yayi saranda ta ci tura.

Ana jin karar manyan bindigogi a birnin Abidjan, yayin da dakaru masu goyon bayan Alassane Ouattara - mutumen da kasashen duniya suka yi amunnar shine ya lashe zaben shugaban kasar na watan Nuwamba - ke cigaba da kaiwa gidan Laurent Gbagbo hari.

Bangaren mista Gbagbo ya ce yunkuri ne na neman hallaka shi.

To amma jami'an Alassane Ouattara sun ce, sun ba dakarunsu umurnin su kamo Laurent Gbagbo din da ransa.

Babban mai gabatar da kara a kotun duniya mai shari'ar mugayen laifufuka, Luis Moreno Ocampo, ya ce yana shirin soma bincike a kan abinda ya kira: kisan kare dangin da aka tsara a Cote d'Ivoire.