Hukumar INEC na taro akan zabe mai zuwa

Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC
Image caption Parfesa Attahiru Jega, shugaban INEC

Shugaban hukumar zaben Najeriya, Parfesa Attahiru Jega, yana ganawa da kwamishinonin zabe na jihohin kasar 36, don tsara yadda za a tinkari zabubukan 'yan Majalisun Tarayya na ranar Asabar mai zuwa.

Ana sa ran cewa, a karshen taron wanda ake yinsa a asirce a Abuja, za a cimma matsaya kan ko za a gudanar da zaben Majalisun Dokokin a wasu jihohi, inda aka sami rahotannin cewa ba a sa alamun wasu jam'iyu ba, a takardun kada kuri'a na 'yan takarar Majalisun dattawa.

A ranar Asabar da ta wuce ce aka shirya gudanar da zaben, to amma sai aka dage shi, saboda wasu matsalolin da aka fuskanta, wadanda suka hada da rashin isar kayayakin aiki, da ma'aikatan zabe.