Jiragen kawance sun kai hari kusa da Misurata a Libiya

Magoya bayan Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Magoya bayan Kanar Gaddafi

Jiragen yakin Birtaniya dake cikin farmakin da kungiyar tsaro ta NATO ke kaiwa a Libya, sun kai hari a kan wasu wuraren soji a kusa da birnin Misrata.

Jami'ai sunce tankokin yakin gwamnatin Libya 6, da motoci masu sulke 6 ne aka ragargaza a kusa da Misrata da kuma birnin Sirte.

Kungiyar NATO ta ce za ta yi iyakacin kokarin ta domin kare fararen hula a Misrata, bayan kakkausar sukar da shugabannin 'yan tawaye suka yi mata.

A jiya wani kwamandan 'yan tawayen ya ce, Misrata za ta kau daga doron kasa, muddin dai kungiyar tsaron ta NATO ba ta dauki mataki ba.

Tun farko dai ministan harkokin wajen Faransa, Alain Juppe, ya ce mutanen Misrata na bukatar taimakon gaggawa.